Libya

Hare-haren sojin Haftar sun hallaka tarin jama'a a Tripoli

Dakarun sojin Khalifa Haftar
Dakarun sojin Khalifa Haftar ©REUTERS/Esam Omran Al-Fetori

Hare-hare ta sama da mayakan Khalifa Haftar suka kai kan birnin Tripoli sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 4 tare da raunata wasu akalla 20 dukanninsu fararen hula.

Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar lafiya a Libya, Amin al-Hachemi, ya ce adadin mamatan zai iya karuwa, lura da cewa mafi yawan wadanda aka kwantar a asibiti, sun samu munanan raunuka ne.

Wannan dai ne karon farko da dakarun Haftar ke kai farmaki ta sama cikin mako 3 da suka shafe suka kai farmaki don ganin sun kwace iko da birnin Tripoli da ke karkashin gwamnati mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ja hankalin bangarorin biyu masu da'awar shugabancin kasar da su kawo karshen rikicin don samun damar tseratar da tarin fararen hula da hare-harensu ke ritsawa da su.

Cikin mako 3 da dawowar rikicin rahotanni da nuni da cewa adadin wadanda suka mutu ya tasamma 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI