Kamaru ta lashe kofin Afrika na 'yan kasa da shekaru 17
Wallafawa ranar:
Tawagar kungiyar kwallon kafar Kamaru ta ‘Young Indomitable Lions ta lashe kofin Afrika na ‘yan kasa da shekaru 17 bayan lallasa takwararta ta Guinea Syli Cadets da kwallaye 5 da 3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, yayin wasan da ya gudana jiya a birnin Der as Salam na Tanzania.
Kungiyoyin biyu dai sun yi canjaras ne a tsawon lokacin da aka dibar musu matakin da ya tilasta basu damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, wanda kuma Kamarun ta yi nasara, a gasar wadda aka shafe mako 2 ana yi.
Kafin rashin nasara a hannun Kamaru, Guinea ta lallasa tawagar Najeriya ta Gne da kwallaye 10 da 9 shi ma dai a bugun daga kai sai mai tsaron ragar a shekaran jiya Asabar, yayinda itama Kamaru ta lallasa Angola ne a wasan ta na gab da na karshe.
Wannan dai ne karo na 2 da Kamaru ke samun nasarar dage kofin gasar cin kofin na Afrika amma fa na ‘yan kasa da shekaru 17.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu