Njaeriya-PDP-Buhari

PDP ta zargi Buhari da sace Naira Tiriliyan 14 cikin shekaru 4

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari AFP

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta zargi shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari da sace Naira tiriliyan 14 cikin shekaru hudun farko da ya yi kan mulki.

Talla

Wata sanarwa da sakataren yada labaran Jam’iyyar Mr Kola Ologbondiyan ya fitar a karshen mako ta yi zargin cewa, tsoron bankado badakalar satar tarin kudaden ne ya tilastawa Muhammadu Buhari neman sake ci gaba da wanzuwa a mulki zuwa shekaru 4 masu zuwa.

Sanarwar ta PDP ta ce kudaden da gwamnatin Buharin ta wawure sun hadar da Naira Tiriliyan 9 daga Ma’aikatar man fetur din kasar kana da ma wasu triliyan 1 da biliyan dari 4 na tallafin man fetur da gwamnatin ta yi ikirarin cirewa sai kuma Naira Tiriliyan 1 da biliyan dari daya na danyen man fetur da gwamnatin ta sayarwa wasu kamfanoni marasa rijista ba kuma tare da ta sanya kudin a lalitar gwamnati ba.

Sanarwar PDP ta ci gaba da cewa akwai Naira biliyan 33 da aka wawure daga cikin kudin da aka warewa hukumar agaji ta NEMA kana wasu biliyan 18 wanda bangare ne na biliyan 48 da Majalisar zartaswa ta amince da warewa don kula da ‘yan gudun hijira a jihohin Borno Yobe da kuma Adamawa.

Ka zalika sakataren jam’iyyar ta PDP Mr Kola Ologbondiyan ya kuma yi ikirarin cewa adadin kudin da Najeriya ta ciwo bashi shi ne mafi muni a tarihi, inda yanzu haka ake bin gwamnatin Buharin bashi Naira tiriliyan 24 da biliyan dari 3 da tara.

A cewarsa cikin shekaru 3 gwamnatin Muhammadu Buhari mai ikirarin kawo sauyi a Najeriyar ta ranto kudin da yawansu ya kai tiriliyan 24 da rabi, ba kuma tare da wani gamsasshen aiki guda daya da talakawan kasar za su amfana ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.