Uganda-Bobi

Kotun Uganda ta yi umarnin ci gaba da tsare Bobi Wine

Dan Majalisa Robert Kyagulanyi, da aka fi sani da Bobi Wine a Uganda
Dan Majalisa Robert Kyagulanyi, da aka fi sani da Bobi Wine a Uganda AFP PHOTO/Michele SIBILONI

Alkalin kotu a Uganda, ya bayar da umarnin ci gaba da tsare Bobi Wine shahrarren mawaki kuma dan majalisar dokoki da ya yi kaurin suna wajen sukar lamirin shugaban kasar Yuweri Museveni.

Talla

A cikin makon jiya ne jami'an 'yan sandan kasar suka kame Bobi Wine tare da wasu mutane biyar masu mara masa baya, lokacin da ya ke shirin gabatar da wani wasa a birnin Kampala.

Mahukunta a kasar ta Uganda dai na zargin Bobi Wine da shirya gangami ba tare da sanar da hukumomin tsaro ba.

A cikin shekarar da ta gabata ‘yan sanda sun taba kama dan majalisar tare da yi masa duka har sai da aka kwantar da shi a asibiti, saboda makamancin laifin na shirya gangamin kalubalantar gwamnati ba tare da neman izinin mahukunta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.