Sudan-Zanga-Zanga

Bangaren Soji da farar hula na takaddama kan mukamai a Sudan

Wasu masu zanga-zanga a Sudan
Wasu masu zanga-zanga a Sudan ©REUTERS/Umit Bektas

An gaza cimma daidaito kan yadda ya kamata a raba mukamai tsakanin sojin Sudan da kuma fararen hular da ke jagorantar tarzomar da ta yi sanadiyyar kawar da shugaba Omar al-Bashir.

Talla

A daidai lokacin da ake dakon fitar sanarwa dangane da yadda sabuwar gwamnatin za ta kasance ne, sai kakakin Majalisar Mulkin Sojin Laftana Janar Shamsuddine Kabbashi ya sanar da manema labarai cewa har yanzu akwai sauran batutuwan da ba kammala warwarewa ba a tsakaninsu.

Sai dai har yanzu al'ummar Sudan na ci gaba da zanga-zanga domin ganin an mika ragamar mulkin kasar a hannun farar hula.

A baya-bayan nan ne dai aka samu matsaya tsakanin bangaren sojin da suka hambarar da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir da kuma jagororin fararen hula wanda ta kai ga cimma matsayar rarraba mukamai gabanin mika mulkin dungurum ga fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI