Najeriya-Buhari

'Yan adawar Benin sun nemi Talon ya gaggauta soke sakamakon zabe

Tsohon shugaban kasar Benin Nicephore Soglo lokacin da ya ke fitowa daga taron bangarorin adawa a birnin Cotonou
Tsohon shugaban kasar Benin Nicephore Soglo lokacin da ya ke fitowa daga taron bangarorin adawa a birnin Cotonou Yanick Folly / AFP

‘Yan adawa a Jamhuriyar Benin sun bai wa shugaban kasar Patrice Talon wa’adin yinin yau talata, domin ya sanar da jingine zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da da aka gudanar shekaran jiya lahadi.

Talla

Yayin wani taron bangarorin adawar da ya gudana a birnin Cotounou, tsohon shugaban kasar Nicephore Soglo ya gabatar da jawabai gaban manema labarai da ke nuna cewa, dole ne a jingine sakamakon zaben, wanda ya gudana ba tare da jam’iyyar adawa ba.

A jawaban na sa tsohon shugaban kasar ta Benin Soglo, ya fara da jinjina ga al’ummar kasar wadanda ya ce sun jajirce wajen nunawa shugaba Talon cewa zaben da ya shirya bai kai ga samun nasara ba.

Sai kuma ya ci gaba da cewa ‘‘Muna son shugaban ya fahinci cewa ya yi kuskure, amma a shirye muke domin gafarta masa, ya kamata ya dakatar da wannan batu na zaben ‘yan majalisa, domin kuwa cigaba da hakan abu ne da zai iya kawo karshen mulkinsa.’’

‘‘Muna kira a gare shi ya bude tattaunawa domin samar da sulhu, da kuma gudanar da tsaftaccen zabe irin na dimokuradiyya’’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI