Najeriya-MDD

Yawan Al'ummar Najeriya ya kai miliyan 201 a yanzu -MDD

Wani dandazon 'yan Najeriya
Wani dandazon 'yan Najeriya Reuters

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewar adadin al’ummar Najeriya yanzu haka ya kai miliyan 201 sabanin miliyan 180 da hukumomin kasar ke ikrari a baya.

Talla

Wani rahotan Hukumar kula da yawan jama’a na Majalisar da aka gabatar, ya nuna cewar adadin 'yan Najeriya ya tashi daga miliyan 180 zuwa miliyan 201.

Majalisar ta ce yayin da Najeriya ke da mutane miliyan 201 makotan ta irin su Nijar na da miliyan 23.2, Jamhuriyar Benin na da miliyan 11.8, Chadi na da miliyan 15.8 sai kuma Kamaru mai miliyan 25.3.

Rahotan Majalisar ya bayyana cewar, 'yan Najeriya na rayuwa ne zuwa shekara 55, yayin da jarirai 814 ke mutuwa wajen haihuwa daga kowanne 100,000 da ake haifa.

Majalisar ta ce kashi 32 na mutanen Najeriya na shekaru ne tsakanin 10 zuwa 14, yayin da masu shekaru tsakanin 15 zuwa 64 ke kashi 54, kana masu sama da shekaru 65 kuma ke kashi 3 kacal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.