Najeriya-Zamfara-Katsina

Najeriya za ta aike da karin jiragen yaki Zamfara da Katsina

Wasu dakarun sojin saman Najeriya a Maiduguri
Wasu dakarun sojin saman Najeriya a Maiduguri Reuters

Rundunar Sojin saman Najeriya ta na shirye shiryen aikewa da karin jiragen shalkwafta na yaki kirar Agusta 109 zuwa jihohin Zamfara da Katsina masu fuskantar matsalar hare-haren ‘yan bindiga.

Talla

A cewar wata majiyar rundunar sojin Najeriyar za a aike da jiragen ne bayan bikin cika shekaru 55 da kafuwar rundunar sojin saman da zai gudana alitinin mai zuwa, a matsayin wani sabon yunkuri don kammala murkushe ‘yan bindigar da ke haifar da barazanar tsaro a jihohin biyu.

Yayin wata zantawar jaridar PUNCH da kakakin rundunar sojin saman Najeriyar Air Commodore Ibikunle Daramola ya tabbatar da cewa baya ga jiragen akwai kuma tarin dakaru da za a sake aikewa jihohin don kawo karshen hare-haren ‘yan bindigar.

Haka zalika kakakin na rundunar sojin saman Najeriyar Daramola, ya ce za kuma a bude wata shalkwata ta musamman a birnin Gwari da za ta rika kula da dakaru da kuma jiragen da ke yaki a jihohin ciki har da kadunar mai fama da hare-haren ‘yan bindiga da ayyukan masu garkuwa da mutane don kudin fansa.

Kakakin na Rundunar sojin saman Najeriyar ya ce Babban Hafson sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar, tare da Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai ne za su kaddamar da shalkwatar a yau Asabar.

Hare-haren 'yan bindiga, garkuwa da mutane satar shanu da kuma rikicin kabilanci dai na ci gaba da ta'azzara a jihohin Katsina Zamfara da jihar Kaduna, inda a kowacce rana tarin jama'a kan rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI