Sudan

Sudan: Masu shiga tsakani sun bukaci kafa majalisa 2

Laftanar Janar Omar Zain al-Abdin, shugaban majalisar sojojin Sudan da ke rikon mulkin kasar. 12/4/2019.
Laftanar Janar Omar Zain al-Abdin, shugaban majalisar sojojin Sudan da ke rikon mulkin kasar. 12/4/2019. AFP/ A. Shazly

Masu shiga tsakani domin sasanta sojojin dake mulki a Sudan da kuma shugabannin masu zanga-zanga sun gabatar da shawarar kasar ta samu majalisar mika mulki guda biyu.

Talla

A karkashin tsarin, sojoji za su jagoranci majalisa guda, dayar kuma fararen hula su jagorance ta.

Sai dai Omar al-Digeir, daya daga cikin shugabannin masu zanga-zangar yace har ba a cimma matsaya kan batun ba, da kuma rawar da kowacce majalisa za ta taka.

Majalisar sojojin kasar ta bayyana karara cewar ba za ta mikawa fararen hular mulki ba, koda yake wani lokaci a yau Litinin ake sa ran gwamnatin sojin ta Sudan za ta fitar da cikakken bayani kan makomar tafiyar da mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.