Isa ga babban shafi
Ghana

Ghana ta kame jagororin masu yunkurin ballewa daga Kasar

Wasu Jamu'an tsaro a Ghana
Wasu Jamu'an tsaro a Ghana Daniel Finnan

'Yansanda a kasar Ghana sun sanar da kama mutane akalla 81 da ake zargin su da yunkurin ballewa domin kafa kasa ta kan su aYankin Gabashin kasar. Wannan ya biyo bayan kama shugabannin su guda 8 ranar lahadi.

Talla

Rundunar 'yansandan ta Ghana ta ce ta yi nasarar kame mutanen ne a garin HO mai nisan kilomita 150 daga arewa maso gabashin kasar, bayan gano kokarinsu na yunkurin ballaewa, don kafa kasa mai cin gashin kanta da suka sanyawa suna Western Togoland.

Kamen dai na zuwa ne bayan makamancinsa a ranar Lahadi, da ya kai ga kame jagororinsu wadanda yanzu haka ake tuhuma da cin amanar kasa baya ga horar da wasu dakaru na musamman.

Wata majiyar 'yansanda ta shaidawa manema labarai cewa a halin yanzu sun yi nasarar kame mutane 20, kuma suna sa ran kama wasu nan gaba a binciken da suke cigaba da gudanarwa.

Majiyar ta ce wadanda aka kame mambobin wata gidauniyar nazari ce ta Homeland study group foundation, wadda suka kafa a shekarar 1994, a kokarinsu na kafa kasar Western Togoland.

Ko a shekarar 2017 an kame jagororin kungiyar tare da yi musu gargadi kada su yi wani abu da zai sabawa dokar Kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.