Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyyar Condo-Ebola

Majalisar Dinkin Duniya ta dauki sabbin Matakan yaki da Ebola a Congo

Wasu jami'an lafiya da ke kula da masu cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
Wasu jami'an lafiya da ke kula da masu cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Photo: John Wessels/AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta na kara daukar matakai kan yadda za’a dakile cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, ganin yadda cutar ta kwashe watanni 10 ta na kashe jama’a.

Talla

Sakatare Janar Antinio Guterres ya bayyana damuwa kan irin yawan mutanen da suka rasa rayukan su, yayin da ya yabawa ma’aikatan lafiyar da ke kula da masu dauke da cutar.

Magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya Antinio Guterres duk da bai fayyace sabbin matakan yaki da Ebolar kai tsaye ba, amma ya ce sun shirya tsaf don kammala fatattakar cutar wadda kawo yanzu ta hallaka fiye da mutum dubu guda a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da ke fuskantar barkewar cutar karo na 10 a tarihi.

Ko a makon da ya gabata, cutar a hallaka har da jariri mai watanni 6 da haihuwa, duk kuwa da rigakafi da kuma magungunan yaki da cutar da hukumomin lafiya na duniya ke samarwa.

A bangare guda hare-hare kan cibiyoyin kula da masu cutar ta Ebola na matsayin babban kalubale ga yunkurin yaki da cutar wanda a lokuta da dama kan rutsa da likitocin da ke bayar da kulawa ga marasa lafiyan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.