ANC ta sake samun nasara a zaben Afrika ta kudu da karancin rinjaye
Wallafawa ranar:
Jam’iyyar ANC a Afrika ta kudu ta sake nasarar lashe babban zaben kasar da ya gudana cikin makon jiya, sai dai wannan ne mafi munin sakamako da ta taba samu a tarihi wanda ke da alaka da zarge-zargen rashawa da kuma nuna wariyar launin fata da ya dabaibaye gwamnati mai ci.
Sakamakon dai ya nuna ANC ta samu kasa da kashi 60 na kuri’un da aka kada, duk kuwa da matsayinta na wadda ta jagoranci kasar tun bayan juyi-juya halin 1994 da ya kawo karshen tasirin farar fata a kasar karkashin jagorancin Nelson Mandela.
Sai dai duk da hakan ANC ta samu isasshen kujeru a majalisa da za su bai wa shugaba Cyril Ramaphosa damar ci gaba da jagoranci kasar har zuwa nan da shekaru 5 masu zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu