MDD ta yi taro na musamman kan matsalar tsaron yankin Sahel
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kwana guda bayan kazamin harin da aka kai Jamhuriyar Nijar da ya hallaka sojojin kasar 28, Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da taro na musamman kan tabarbarewar tsaro a yankin Sahel.
Ministan harkokin wajen Burkina Faso da ya halarci taron, Alpha Barry, ya bukaci kafa wani sabon kawancen duniya domin ceto yankin Sahel daga barazanar ‘yan ta’adda.
Barry ya ce tun bayan kafa rundunar sojin hadin gwiwa ta G5 Sahel da suka yi, kasashen da ke kawacen da suka hada da Chadi, Mali, Mauritania, Nijar da kuma Burkina Faso, suna ware akalla kashi 18 zuwa 32 na kasafin tattalin arzikinsu a duk shekara wajen tallafawa, rundunar hadin gwiwar.
Ministan ya kuma bukaci majalisar dinkin duniya ta gaggauta daukar matakan kawo karshen yakin kasar Libya, la’akari da cewa, yana bada muhimmiyar gudunmawa wajen karawa masu da’awar Jihadi da kuma sauran ‘yan bindiga karfi a yankin na Sahel.
A farkon shekarar 2019 kadai, sama da mutane 300 ne suka hallaka, sakamakon hare-haren ta’addancin da aka kai a sassan yankin na Sahel.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu