Afrika

Wani sojan Najeriya a Mali ya rasu

Wasu daga cikin dakaru dake fada da yan Jihadi a yankin Sahel
Wasu daga cikin dakaru dake fada da yan Jihadi a yankin Sahel RFI

Wasu jerry hare-hare da ake zargin mayakan jihadi da kaiwa zuwa ayarin dakarun wanzar da zaman lafiya a Mali musaman garuruwan Timbouktou da Tessalit dake arewacin kasar sun yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin sojan rundunar dan asalin kasar Najeriya

Talla

Sanarwar da Sakatary Majalisar Dimkin Duniya ya fitar na Allah wadai da harin ,tareda bayyana cewa sojin da ya samu rauni ya rasu ne a Timbouktou, haka zalika daf da garin Tessalit dake yankin Kidal wasu sojojin wanzar da zaman lafiya yan kasar Chadi uku sun samu rauni a dai dai lokacin da motar silke da suke cikin ta ta taka nakiya.

Antonio Gutteres ya na mai kira zuwa hukumomin Mali don ganin sun bayar da hadin kai don zakulo wandada ke da hanun a kisan sojan wanzar da zaman lafiya da kuma hukunta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI