Isa ga babban shafi
Afrika

Yan Majlisu za su gurfana a Madagascar

Gwamantin Shugaba Andy Rajoelina na Madagascar
Gwamantin Shugaba Andy Rajoelina na Madagascar GREGOIRE POURTIER / AFP
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

A Madagascar,hukumar dake da nauyin yaki da ayukan da suka jibancin bayar da cin hanci da kuma karbar rashawa Blanco ta mika zuwa kotu sunayen wasu daga cikin yan Majalisar kasar da suka karbi na goro, makonni biyu kafi a je zaben yan majalisun kasar.

Talla

Hukumar da ta share kusan shekara daya ta na bincike ta zakulo sunayen yan majalisu 79 da kuma ake sa ran kotu za ta yi aikin ta a kai.

Jam’iyyun adawa na zargin wasu daga cikin yan majalisun da karbar kusan milyan 50 na ariry kudin kasar .

Shugaban kasar a lokacin karbar rantsuwar soma aiki ya dau alkawali na yaki da cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.