Batun tantance 'yan jaridu a majalisar Najeriya ya janyo cece-kuce
Wallafawa ranar:
Hukumar gudanarwar majalisar dokokin tarayyar Najeriya ta fidda sabbin ka’idoji na tantance ‘yan jarida da za su rika shiga majalisa daukan labarai. Wannan lamari ya janyo tutsu daga dukkannin kungiyoyin ‘yan jarida dama ‘yan jaridar kasar, inda duka suke cewa ba za ta sabu ba.Wasu daga cikin ka’idoji 13 da majalisar ta fitar sun hada da,dole dan jarida ya nuna takardar shaidan inda ya ke aiki na biyan haraji, dole jarida yazama ta na saida guda 40,000 mafi karanci kowace rana, 'yan jadidan kasa shen waje kamar su RFI, sai hukumar harkokin kasashen waje na Najeriya ta tantance, su da dai sauransu. Ga wakilinmu na Abuja Mohammed Sani Abubakar dauke da rahoto.
Batun tantance 'yan jaridu a majalisar Najeriya ya janyo cece-kuce
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu