Mali-Sahel

'Yan Mali na zanga-zanga kan sauya mazaunin shalkwatar G5 Sahel

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Bamako fadar gwamnatin kasar Mali, inda su ke nuna rashin amincewarsu da yunkurin dauke shalkwatar rundunar tsaron G5-Sahel daga Mopti zuwa birnin na Bamako.

Wasu dakarun sojin Mali
Wasu dakarun sojin Mali RFI
Talla

Masu zanga-zangar cikinsu har da matan sojojin da suka rasa rayukansu a fagen daga, sun ce bai kamata a dawo da shalkwatar rundunar birnin Bamako ba, a maimakon haka, ana bukatar ta ne a arewacin kasar inda ake da kungiyoyi masu dauke da makamai.

Tsakiyar kasar ta Mali dai nan ne ke da galibin matsalar tsaron da kasar ke fuskanta ta fuskar hare-hare kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

Ko a farkon watan nan sai da wasu hare-haren kungiyoyin ya hallaka tarin fararen hula a kasar baya ga kisan wasu sojojin hadaka da ke sintiri a dazukan da ake zargin mayakan na Jihadi na samun mafaka a cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI