Afrika

Takaddama ta kaure tsakanin kasashen Uganda da Rwanda

Uganda/Rwanda: rikici na ci gaba tsakanin kasashen biyu dake makwabtaka da juna (16/05/2019)
Uganda/Rwanda: rikici na ci gaba tsakanin kasashen biyu dake makwabtaka da juna (16/05/2019) Dr MEDDY

Yanzu haka takaddama ta kaure tsakanin kasashen Uganda da Rwanda sakamakon zargin da Uganda tayi cewar sojojin Rwanda sun kutsa kai cikin kasar ta inda suka kashe mata mutane guda biyu.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Uganda ta bayyana matakin a matsayin babban abin damuwa wanda ya haifar da kisan kai.

Gwamnatin Uganda ta bayyana matukar bacin ran ta da aukuwar lamarin wanda ya haifar da kutsa kai cikin iyakokin ta.

Sai dai ministan harkokin wajen Rwanda Richard Sezibera yayi watsi da zargin wanda ya bayyana shi a matsayin labarin kanzon kurege.

Danganta tsakanin shugaba Paul Kagame na Rwanda da Yoweri Museveni da suka taimakawa juna wajen hawa karagar mulki tayi kamari, inda suke zargin junan su da yunkuri kisan kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI