Libya

Libya: Sabon gumurzu ya tilastawa mutane sama da dubu 75 tserewa

Kwamandan dakarun Libya Janar Khalifa Haftar, yayin ganawa da manema labarai a birnin Benghazi.
Kwamandan dakarun Libya Janar Khalifa Haftar, yayin ganawa da manema labarai a birnin Benghazi. Reuters

Janar Khalifa Haftar da dakarunsa ke rike da muhimman yankunan kasar Libya, ya ce ba ya da niyyar shiga tattaunawa da mahukuntan birnin Tripoli masu samu goyon bayan majalisar dinkin duniya.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai a farkon makon nan, Janar Haftar, ya sha alwashin ci gaba da kai farmaki har sai zuwa lokacin da sojojin gwamnatin kasar ta Libya da ke Tripoli, wadanda ya kira da sunan ‘yan bindiga suka ajiye makamansu.

Haftar ya shaida wa jaridar 'Journal Dimanche' da ake bugawa a Faransa cewa, ya ce babu laifi a samar da mafita a siyasance ga rikicin kasar ta Libya, amma ba zai shiga tattaunawar ba, har sai zuwa lokacin da ya kakkabe mayakan sa-kai daga yankin baki daya.

Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar a baya bayan nan ya nuna cewa, sabon fadan da ya barke tsakanin sojin gwamnatin Libya mai samun goyon bayan majalisar dinkin duniya, da dakarun Khalifa Haftar, ya tilastawa mutane sama da dubu 75,000 tsrewa daga muhallansu, yayinda wasu 510 suka hallaka.

Hukumar ta WHO ta ce adadin mutanen da suka jikkata sakamakon sabon fadan kuwa ya haura dubu 2 da 400, yayinda kuma ake fargabar fadan ya ritsa da wasu mutanen da adadinsu ya kai dubu 100 a wasu kauyuka da ke wajen birnin Tripoli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI