Najeriya

Shirin bunkasa noman rani a jihar Kano da Ke Najeriya

Nigeria-Madatsar ruwan Bakalori a jihar Sokoto
Nigeria-Madatsar ruwan Bakalori a jihar Sokoto RFIHAUSA/Faruk Yabo

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani bincike da zai lakume makudan kudade domin kawar da wasu sinadarai na kanwa da gishiri da ke barazana ga gonakin noman rani a Jihar Kano da ke arewacin Kasar.Aikin binciken ya biyo bayan korafe-korafen da manoma ke yi dangane da illar wadannan sanadarai ga amfanin gona, wanda suka ce al’amarin ya tasamma zama barazana ga yunkurin samar da wadataccen abinci a kasar.Wakilinmu na Kano Abubakar Abdulkadir Dangambo ya aiko mana rahoto a game da wannan shiri.