Afrika

Za a gudanar da zaben yan Majalisu a Chadi a cikin shekarar 2019

Majalisar dokokin Chadi
Majalisar dokokin Chadi © RFI/Aurélie Bazzara

A kasar Chadi Shugaban hukumar gudanar da zabe (CENI), Kodi Mahamat Bichara, ya tabbatar da cewa, shekara ta 2019 zata kasance shekarar gudanar da zaben ‘yan majalisu da kananan hukumomi .An dai share dogon lokaci ana dage zaben na kasar ta Chadi.

Talla

Shugaban hukumar zaben kasar ya yi alƙawarin sanar da ranar da za a gudanar da zaɓen a cikin kwanaki masu zuwa.

Bayan wannan bayanin nasa wasu 'yan kasa sun fara tofa albarkacin bakinsu kan gudanar da zabe cikin adalci kamar dai yada zaku ji a wannan rahoto da wakilinmu a kasar Chadi Tijjani Mustapha Mahdi ya aiko mana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.