Gawar Etienne Tshisekedi ta isa birnin Kinshasa
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jirgin da ke dauke da gawar tsohon madugun 'yan adawar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo Etienne Tshisekedi ya isa birnin Kinshasa a wannan alhamis, inda ake shirin yi masa jana'iza irin ta karramawa.
Tshisekedi, ya rasu ne cikin watan fabarairun shekara ta 2017 a birnin Brussels na kasar Belgium, lokacin da ya je kasar domin duba lafiyarsa, kuma tun a wancan lokaci ne ake kokarin dawo da gawarsa gida domin yi ma ta jana’iza sai a wannan lokaci.
An dai samu rabuwar kawuna ne tsakanin iyalan marigayin da kuma tsohuwar gwamnatin Shugaba Joseph Kabila kan yadda za a dawo da gawar da kuma yadda ya kamata a yi ma ta jana’iza.
To sai dai a zaben da aka yi farkon wannan shekara, dan Tshisekedi, wato Felix Tshisekedi ya yi nasarar lashen zaben shugabancin kasar ta Congo, inda ya sa ya gaggauta dawo da gawar mahaifin nasa daga Belgium domin yi ma ta jana’iza a cikin kasar ta Congo.
An baje akwatin gawar daga yau juma'a har zuwa gobe asabar domin bai wa jama'a damar yi ma ta bankwanan karshe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu