kamaru

Shugaban 'yan awaren Kamaru ya amince da tattaunawa

Karon farko, Sisiku Ayuk Tabe, jagoran ‘yan awaren da ke neman kafa kasar Ambazonia daga cikin Kamaru, ya a shirye yake ya shiga tattaunawa da mahukuntan birnin Yaounde, amma da sharadi.

Shugaban Kamaru Paul Biya, na jawabi a ranar 3,disamba, 2018.
Shugaban Kamaru Paul Biya, na jawabi a ranar 3,disamba, 2018. RFI/Capture d'écran
Talla

A wasikar da ya rubuta daga inda ake tsare da shi ranar 27 ga wannan wata, Sisiku Ayuk Tabe, ya gindaya sharudda har guda 7, da suka hada da sakin illahirin magoya bayansa da ke tsare saboda rikicin yankin na ‘yan aware, sai kuma janye sojoji da ma sauran wakilan gwamnatin Kamaru da suka hada da kantomomi, gwamnoni da dai sauransu da aka tura zuwa yankunan da ‘yan awaren ke kira kasar Ambazonia.

Jagoran ‘yan awaren ya ce wadanda za su halarci teburin tattaunawar kuwa za a kira su ne da sunan wakilan Jamhuriyar Kamaru da kuma na kasar Ambazonia, sai kuma MDD, Birtaniya da kuma Faransa a matsayin ‘yam kallo.

Wani sharadi da jagoran ‘yan awaren ya gindaya shi ne, dole ne wannan tattaunawa ta gudana a wani gari da ke matsayin dan ba ruwanmu game da rikici, ko dai birnin New York, ko Geneva ko kuma shalkwatar kungiyar tarayyar Afirka a cewarsa.

Sannan kuma Sisiku Ayuk, ya ce a dole ne ya kasance a samu daidaiton wakilcin tsaknin bangarensa da na gwamnati a wannan tattaunawa, sannan kuma batutuwa uku ne za a mayar da hankali a kai, da suka hada da siyasa, tattalin arziki da kuma zamantakewar al’umma.

A cikin watan janairun 2018 ne aka cafke Ayuk a Najeriya, tare da tasa keyarsa zuwa kasar ta Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI