Bakonmu a Yau

Yarjejeniyar kasuwancin bai-daya tsakanin kasashen Afirka ta fara aiki

Wallafawa ranar:

A wannan alhamis 30 ga watan mayu, shirin kungiyar kasashen Afirka na samar da kasuwar bai-daya tsakanin kasashe 54 da ke nahiyar ya fara aiki, duk da yake kasashe 22 kawai ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu.Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na kungiyar, Albert Muchanga ya ce akalla mutane biliyan daya da miliyan 200 za su amfana da kasuwar.Kuma a ranar 7 ga watan Yuli za’a kaddamar da ita a taron AU da zai gudana a Nijar.Domin sanin tasirin kasuwar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Dr Dauda Muhammed Kontagora, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

Bikin sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci ta bai-daya tsakanin kasashen Afrika a birnin Kigali na Rwanda
Bikin sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci ta bai-daya tsakanin kasashen Afrika a birnin Kigali na Rwanda © REUTERS/Jean Bizimana