Ana tsare da wasu magoya bayan Kamto a Kamaru
Wallafawa ranar:
A Kamaru akalla magoya bayan dan adawa Maurice Kamto da ya kasance na biyu a zaben Shugabancin kasar 300 ne aka kama bayan kazamar zanga-zanga da ta gudana a wasu biranen kasar ta Kamaru.
Magatakardar jam’iyyar MRC ta dan adawa Maurice Kamto ya bayyana wasu biranen kasar da suka hada da Yaounde , Douala, Bafoussam da Nkongsamba inda aka yi ta kama magoya bayan su, daga ciki harda mataimakin shugaban jam’iyyar Mamadou Mota.
Ya zuwa hukumomin Kamaru basu ce upon ba dangane da batun tsare wasu magoya bayan jam’iyyar adawa da a yan Sanda ke yi yanzu haka, yayinda lauyoyin dake kare jam’iyyar adawa suka aike da wasika zuwa majalisar dimkin Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu