Najeriya

Buhari zai jagoranci taron kasashen yankin Tafkin Chadi

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. Reuters/AFOLABI SOTUNDE

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce zai jagoranci taro da shugabannin kasashen yankin Tafkin Chadi, domin tattaunawa kan halin da sha’anin tsaro ke ciki a yankin.

Talla

Shugaban, ta hannun kakakinsa malam Garba Shehu, yace taron zai gudana a dai dai lokacin da ake bukukuwan ranar Dimokaradiyya ta Najeriya da kuma murnar rantsar da sabuwar gwamnati a Abuja, ranar 12 ga watan Yuni da muke ciki.

Sanarwar da kakakin shugaban na Najeriya ya fitar, ta ce Buhari da takwaransa na kasar Chadi Idris Deby suka tsaida lokacin taron kasashen na yankin Tafkin Chadi, yayin ganawa a Makkah, inda aka kammala taron kungiyar hadin kan kasashen Musulmi OIC.

Yayin taron na OIC, kungiyar ta sha alwashin taimakawa kasashen Afrika na yankin Sahel, musamman Chadi, Nijar, Najeriya da kuma Kamaru, wajen karfafa tsaro, da murkushe ta’addancin da suke fama da shi, da sauran matsalolin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI