kamaru

Hukumomi a Kamaru sun kame 'yan adawa sama da 350

Maurice Kamto, shugaban jam'iyyar MRC a Kamaru
Maurice Kamto, shugaban jam'iyyar MRC a Kamaru RFI/Capture d'écran

Babbar jam’iyyar adawa a Kamaru, ta ce an cafke magoya bayanta akalla 350 a lokacin zanga-zangar da suka yi ranar asabar da ta gabata a manyan biranen kasar.

Talla

Magoya bayan Maurice Kamto wanda ke tsare a gidan yari tun cikin watan Janairun da ya gabata a birnin Yaounde, sun gudanar da tarzomar ne domin neman a saki jagoran nasu, to sai dai jami’an tsaro sun tarwatsa su tare da kame wasu da dama.

A cewar jam’iyyar MRC ta Maurice Kamto, fiye da magoya bayan ta 350 ne aka kama; 180 daga cikinsu a Yaounde aka kama su, yayin da 100 kuwa aka kama a garin Nkongsamba dake yammacin kasar.

Jam’iyyar ta kara da cewa hukumomin kasar sun hana wadanda suka kama damar daukar lauyoyin da zasu kare su, tare da dakile musu damar samun kula da lafiyarsu.

Tun bayan zaben shugaban kasar Kamaru na watan Oktoban 2018 jam’iyyar MRC take shirya zanga – zanga.

Sakamakon da aka fitar a hukumance ya nuna cewa Kamto ya zo na biyu a zaben, amma MRC ta ce an tafka magudi ta wajen yin aringizon kuri’u, don taimaka wa shugaba Paul Biya wanda ya shafe shekaru 36 yana jan ragamar mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI