Sudan

Kungiyar Tarayar Afrika ta kori kasar Sudan

Jagoran Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan Abdulrahman
Jagoran Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan Abdulrahman RFI

Kungiyar Tarayyar Afrika AU ta kori kasar Sudan daga cikin kungiyar har sai Hukumomin sojan kasar sun maida mulki hannun fararen hula don kawo karshen zubar da jini da ake ci gaba da samu.

Talla

Tun bayan samame da kisan masu zanga-zanga da suka mamaye harabar Babban ofishin Soja dake Khartoum, ake ta kira ga kungiyar Tarayyar Afrika da ta dauki mataki kan sojan Sudan.

Wasu majiyoyin samun labarai na cewa jiya Laraba an tsamo mamata 40 daga kogi, wanda ya kawo yawan mamata da ake zargin sojan kasar sun kashe 108.

Kungiyoyin dake zanga-zangan na cewa ba zasu sake shiga tattaunawar sulhu ba da bangaren sojan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.