Isa ga babban shafi
DR-Congo

Karin mutane 2000 sun kamu da Ebola a Congo - WHO

Jami'en Hukumar Lafiya ta Duniya da na Congo a yankin Kivu
Jami'en Hukumar Lafiya ta Duniya da na Congo a yankin Kivu REUTERS/Samuel Mambo/File Photo
Zubin rubutu: Michael Kuduson
1 Minti

Hukumar lafiya ta duniya ta ce fiye mutane dubu 2 ne aka gano suna dauke da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokaradiyyara Congo, duk da cewa an samu raguwar masu kamuwa da cutar a yankin arewacin Kivu na kasar.

Talla

A Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, ana ta Allah sambarka sakamakon raguwar sabbin masu kamuwa da cutar, musamman ma a Butembo inda cutar ta fi kamari.

Sai dai kuma a lokaci guda, masu kamuwa da cutar karuwa suke a yankin Mabalako, inda ba a ma kai ga gano wasu masu dauke da cutar ba.

Wasu kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa da ke ayyukan agaji a yankin da annobar Ebola ta shafa, sun nuna matukar damuwa kan rashin yarda da al’umma ke ci gaba da nunawa ma’aikatan lafiya, lamarin da ya sa matsalar ta ki ci ta ki cinyewa.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce har yanzu akwai kashi 75 na wadanda suka kamu da wannan cutar da ba a kai ga gano su ba, wadda hakan matsala ce babba ga lafiyar al’umma.

Shugaban sashen bayar da agajin gaggawa na hukumar, Michael Ryan a yayin ganawarsa da kungiyoyi masu zaman kansu, ya ce dole ne a yi aiki tukuru, tare da taka tsan tsan wajen kawo karshen wannan annobar, shi ya sa ma hukumar ke wani kokari na sa ido kan mutane dubu 15 da suka yi cudanya da masu dauke da wannan cutar kafin ya kai ga bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.