Sudan

Jami'an tsaron Sudan sun kame shugabannin 'yan adawa

Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed, yayin ganawa da shugabannin gwamnatin mulkin soji na kasar Sudan.
Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed, yayin ganawa da shugabannin gwamnatin mulkin soji na kasar Sudan. AFP

Jami’an tsaron Sudan sun kame wasu tsaffin ’yan tawayen kasar 2, da kuma jagoran yan adawa 1, kwanaki kalilan bayan tarwatsa masu zanga-zanga da ke neman sojoji su mika mulki ga farar hula.

Talla

A ranar Litinin 3 ga watan Yuni, jami'an tsaron Sudan suka hallaka sama da mutane 100, yayin murkushe masu zanga-zanga da ke zaman dirshan a birnin Khartoum.

Kame tsaffin jagororin yan tawayen da jagoran na yan adawa ya zo ne, sa’o’i kadan, bayan da suka gana da Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed a Khartoum, wanda a jiya Juma’a ya isa birnin domin sansanta shugabannin masu zanga-zangar da bangaren sojoji wajen maido da tattaunawar da suka yi watsi da ita.

Rahotanni sun ce jami’an tsaron kwantar da tarzoma na Sudan da a baya aka fi sani da mayakan Janjawid ne suka kai samamen da aka damke shugabannin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.