Bakonmu a Yau

Malam Nasir Kura na kungiyar Civil Liberty kan taron yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Afirka

Wallafawa ranar:

YAU aka bude wani taron yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Afirka wanda ya mayar da hankali kan yadda za’a dakile amfani da kudaden sata wajen harkokin siyasa da kuma zabe.Taron ya samu halartar shugabannin kasashen Afirka da suka hada da shugaba Buhari na Najeriya, da Paul Kagame na Rawanda da takwarorin su na Ghana da Liberia da Senegal da ake saran suyi jawabi a wajen.Dangane da wannan taro, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Nasir Kura na kungiyar Civil Liberty dake yaki da cin hanci rashawa a Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Reuters/AFOLABI SOTUNDE