Benin

Halin da Benin ke ciki bayan tashin rikin Savè da Tchaourou

Wasu jami'an tsaron Jamhuriyar Benin yayin sintiri a birnin Cotonou.
Wasu jami'an tsaron Jamhuriyar Benin yayin sintiri a birnin Cotonou. AFP / Yanick Folly

Al’ummar garuruwan Save da Tchaourou a wannan Juma’a sun tsinci kansu cikin zaman zulumi, bayan da lamura suka ci gaba da yamutsewa a wasu yankunan biranen da ke Jamhuriyar Benin, bayan shafe kwanaki ana gwabza fada tsakanin 'yan tauri magoya bayan tsohon Shugaban kasar Boni Yayi da kuma jami'an tsaro.Rikicin dai ya samo asali ne daga yadda magoya bayan tsohon shugaban kasar Boni Yayi suka yi kokarin tilastawa jami'an tsaro janye daurin talalar da ake yiwa tsohon shugaban.Abdullahi Isa ya hada mana rahoto dangane da halin da ake ciki.

Talla

Halin da Benin ke ciki bayan tashin rikin Savè da Tchaourou

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.