Najeriya-Zamfara

'Yan bindiga sun hallaka mutane 47 a kauyukan Zamfara 2

Wasu da suka gujewa kauyukansu saboda tsoron hare-haren 'yan bindiga
Wasu da suka gujewa kauyukansu saboda tsoron hare-haren 'yan bindiga rfihausa

A Najeriya, akalla mutane 47 wasu ‘yan bindiga suka hallaka a wani farmaki da suka kai kauyukan Mallamawa da Tungar Kafau da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara cikin tsakaddaren jiya Juma’a.

Talla

Yayin zantawa da sashen hausa na RFI, wani mazaunin garin ya shaida mana cewa ‘yan bindigar sun hallaka mutane 40 a garin Mallamawa yayinda suka hallaka wasu Karin 7 a tungar Kafau.

A cewar shaidan wanda ya nemi a sakaya sunansa, kawo yanzu fargaba ta hana sallatar mutanen da ‘yan bindigar suka kashe saboda tsoron kar su juyo da wani sabon farmaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.