Ebola a Congo ba ta kai matsayin sanya dokar ta baci ba- WHO
Wallafawa ranar:
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta janye matakin sanya dokar ta baci kan annobar cutar Ebolar da ake fuskanta a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, duk da bullar cutar a Uganda cikin wannan makon nan, bisa tsoron ka da dokar ta shafi tattalin arzikin kasar.
Annobar cutar Ebolar a Congo ta baya-bayan nan it ace mafi muni da kasar ta taba fuskanta inda mutane dubu 2 da 108 suka kamu yayinda wasu dubu 1 da 411 suka mutu tun bayan sake bullarta cikin watan Agustan bara.
WHO ta fitar da sanarwar da ke gargadin kasashen da ke makotaka da Congo don su tsaurara matakan kiwon lafiya maimakon daukar matakin sanya dokar ta bacin.
Tun bayan bullar cutar ta Ebola a Uganda cikin makon nan, sanadiyyar shigar wasu mutane 3 daga makociyar kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo yanzu haka mutane 2 sun mutu sakamakon cutar ta Ebola yayinda ake fargabar kamuwar wasu da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu