Najeriya- Afrika ta kudu

Najeriya na neman bahasi kan kisan al'ummarta a Afrika ta kudu

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa Lintao Zhang/POOL Via REUTERS

Shugaban Ofishin jakadancin Najeriya a Afrika ta kudu Mr Godwin Adama ya ce, Ofishin ya shirya tsaf don fara neman bahasi daga jami’an tsaron Johannesburge kan yadda ake gallazawa tare da kisan ‘yan Najeriya a kasar ba tare da daukar mataki ba.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Najeriyar ya ruwaito Godwin Adama na cewa daukar manyan matakai ya zama wajibi la’akari da yadda lamarin ke kara tsananta, bayan kisan ‘yan Najeriyan 130 cikin watanni 30, wanda ya ce adadin na ci gaba da karuwa a kowanne lokaci.

Ko a watannin baya sai da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya mikawa takwarinsa Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudun korafi kan yadda ake yiwa ‘yan Najeriyar Kisan gilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI