Isa ga babban shafi
Masar-Morsi

Kungiyar 'yan uwa musulmi ta zargi gwamnatin Masar da kashe Morsi

Wasu magoya bayan Hambararren shugaban na Masar, Muhammad Morsi, galibi mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brothers
Wasu magoya bayan Hambararren shugaban na Masar, Muhammad Morsi, galibi mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brothers REUTERS/ Mohamed Abd El Ghany
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris | Azima Bashir Aminu
1 Minti

Kungiyar 'yan uwa Musulmi a Masar ta zargi gwamnatin Masar da kashe tsohon shugaban kasa Mohammed Morsi a tsanake.

Talla

Kungiyar ta ce da gangan gwamnati ta tsare shugaban cikin daki ba tare da barin wani ya kai gare shi ba da hana shi magunguna da kuma bashi abinci mara inganci.

Shi ma shugaban Turkiya Recep Tayip Erdogan ya zargi shugaban kama karya na Masar da kashe tsohon shugabana kasar, inda ya ce tarihi ba zai taba mantawa da wadanda suka daure shi ba, kuma suka yi barazanar kashe shi ba.

Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani ya bayyana kaduwar sa da mutuwar Morsi, inda ya aike da sakon ta’aziya ga iyalan sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.