Bakonmu a Yau

Naja'atu Muhammad kan rahoton masu sa ido a zaben Najeriya da ya zargi Jam'iyyu da tunzura jama'a

Wallafawa ranar:

Rahoton masu sa ido kan zaben Najeriya na wannan shekarar ya zargi Jam’iyyun siyasar kasar da tinzura tashin hankalin da ya kai ga rasa rayuka da kuma jikkata jama’a, yayin da rahotan kuma ya zargi jami’an tsaro da kasa daukar matakan kare lafiyar jama’a da kuma dukiyoyin su. Tuni rahotan ya haifar da mahawara daga bangarori daban daban da ke ciki da wajen Najeriya. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Haj Naja’atu Muhammed, kwamishiniya a Hukumar kula da ayyukan Yan Sandan Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

Wani baturen zabe yayin kirga kuri'u a zaben Najeriya na 2019
Wani baturen zabe yayin kirga kuri'u a zaben Najeriya na 2019 REUTERS/Adelaja Temilade