Bakonmu a Yau

Dr Tukur Abdulkadir kan mutuwar tsohon shugaban kasar Masar, Muhammad Morsi a gaban kotu

Wallafawa ranar:

A ranar Litinin Allah ya karbi ran tsohon shugaban kasar Masar Mohammed Morsi a wani Asibiti da ke birnin Cairo.Tsohon shugaban ya fadi ne a cikin kotu, a dai dai lokacin da ake yi masa shari’a.Ganau sun bayyana cewa saida Morsi, 67 yayi ta magana na mintoci 20 gaban alkalin kafin faduwar da yayi.Morsi ne zababben shugaban Masar na farko wanda ya shekara daya yana jagorancin kasar, kafin soja da karfin tsiya su kawar dashi.Dangane da rashin shugaban, da kuma yadda mutuwarsa za ta shafi mulki, da ma siyasar Masar Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dr Tukur Abdulkadir na Jami’ar Jihar Kaduna a Najeriya.

Tsohon shugaban kasar Masar Mohamed Morsi.
Tsohon shugaban kasar Masar Mohamed Morsi. REUTERS