Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru za ta yi makokin sojojinta da Boko Haram ta kashe

Wani sojan Kamaru a bakin gadar Elbeid da ke garin Fotokol. 17/2/2015.
Wani sojan Kamaru a bakin gadar Elbeid da ke garin Fotokol. 17/2/2015. REUTERS/Bate Felix Tabi Tabe
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Kasar Kamaru za ta gudanar da zaman makoki ranar juma’a mai zuwa domin karrama sojojin kasar guda 17 da mayakan Boko Haram suka kashe a harin da suka kai Darak.

Talla

Shugaban kasa Paul Biya ya sanya hannu kan dokar gudanar da zaman makokin domin nuna alhini ga ‘sojojin da suka mutu a daidai lokacin da suke kare kasar su.

Sanarwar tace a ranar juma’ar za’a sauke tutar kasar a Kamaru da kuma ofisoshin jakadancin kasar dake kasashen duniya.

Ministan tsaro Joseph Beti Assomo yace a daren 9 ga watan nan mayakan boko haram sama da 300 dauke da muggan makamai suka kai hari kan dakarun inda suka kashe 17 tare da fararen hula 16, yayin da dakarun suka kasha 64 daga cikin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.