Hukumar yaki da rashawa a Kano ta amsa laifin tuhumar matar Sarki
Wallafawa ranar:
Hukumar da ke sauraron karar jama’a da kuma yaki da cin hanci da rashawa a Kano a Najeriya ta amsa yin kuskure wajen gayyatar uwargidan Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu domin amsa tambayoyi kan binciken da take na kashe kudade ta hanyar da bai kamata ba a Masarautar.
Shugaban hukumar Muhiyi Magaji ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewar lokacin da hukumar ta gano cewar ta aike da takardar gayyata ga uwargidan Sarkin cikin kuskure, ta janye shi kai tsaye.
Rahotanni sun ce labarin gayyatar uwargidan Sarkin, wadda diya ce ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya haifar da zazzafar mahawara a ciki da wajen Kano.
Sai dai Magajki yace Hukumar ta gayyaci mutane wadanda suka bada shaida a gaban ta, kuma zasu cigaba da gayyatar wasu 30 domin cigaba da karbar ba’asi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu