Benin

Yayi Boni ya fice daga Jamhuriyar Benin

Tsohon Shugaban Benin Boni Yayi
Tsohon Shugaban Benin Boni Yayi Yanick Folly / AFP

Tsohon Shugaban Jamhuriyar Benin Boni Yayi a jiya asabar ya bar kasar sa zuwa kasar waje da nufin neman magani, bayan da ya share kusan watanni biyu a tsare bisa umurnin hukumomin Benin da suka girke yan sanda a harabar gidan sa dake birnin Kwatanu a unguwar Cadjehoun

Talla

Wata majiya daga kasar ta Benin na nuni cewa janye jami’an tsaro daga harabar gidan tsohon Shugaban kasarBoni Yayi na zuwa ne biyo bayan ganawa da Shugaban kasar Patrice Talon yayi da Shugaban Najeriya Muhamadu Buhari ,da wasu Sarakunan galgajiya daga Tchaourou mahaifar tsohon Shugaban kasar Yayi Boni.

Tun bayan zaben yan majalisu da ya gudana a kasar ne, jamhuriyar Benin ta fada cikin rikicin siyasa .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.