Isa ga babban shafi

Mutane da Ebola ta kashe a Congo sun haura dubu 1 da dari 5

Yadda ake shirin binne wani da Cutar Ebola ya hallaka a yankin Butembo na Dimokradiyyar Congo ranar 26 ga watan Maris 2019.
Yadda ake shirin binne wani da Cutar Ebola ya hallaka a yankin Butembo na Dimokradiyyar Congo ranar 26 ga watan Maris 2019. REUTERS/Baz Ratner
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu | Ahmed Abba
1 min

Ma’aikatar lafiya a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ta sanar da karuwar mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar annobar cutar Ebolar da kasar ke fuskanta.

Talla

Cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta nuna cewa adadin mutanen da cutar ta hallaka ya karu zuwa mutum dubu 1 da 506 daga watanni goma baya zuwa ranar  Lahadi yayinda yanzu haka ake da mutane dubu 2 da 239 da ke fama da cutar.

Ko cikin watan Yunin nan dai akalla wasu iyalai 2 sun rasa rayukansu a Uganda bayan ziyartar ‘yan uwansu a kasar ta Demokradiyyar Congo.

Kawo yanzu dai akalla mutane dubu 141 aka yiwa rigakafin cutar ta Ebola baya ga jami’an lafiya galibi a yankin gabashin kasar da nan ne annobar cutar ta fi tsananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.