Habasha

An cafke masu juyin mulki a Habasha

An cafke wadanda suka yi kokarin kifar da gwamnatin Amhara a Habasha
An cafke wadanda suka yi kokarin kifar da gwamnatin Amhara a Habasha Zacharias ABUBEKER / AFP

Rundunar sojin Habasha ta cafke akasarin dakarun da  suka yi yunkurin juyin mulki a yankin arewacin kasar.

Talla

A daren ranar Asabar ne wani gungun dakaru karkashin jagorancin janar Asamnew Tsige suka yi yunkurin juyin mulkin a Amhara, daya daga cikin yankuna 9 masu cin gashin kansu a Habasha, inda suka harbe shugaban yankin, Anabchew Mekonnen tare da wani mai ba shi shawara.

A shekarar bara aka saki janar Tsige daga gidan yari bayan shafe shekaru 10 a daure, sakamakon yunkurin juyin mulki a kasar ta Habasha da ya jagoranta a shekarar 2009.

A wani harin na daban duk dai a ranar Asabar, wani mai tsaron lafiyar babban hafsan sojin kasar, Seare Mekonnen ya hallaka mai gidan nasa tare da wani tsohon janar din sojin kasar a birnin Addis Ababa.

Tuni jami’an tsaron kasar suka cafke mai tsaron lafiyar babban hafsan sojin, sai dai har yanzu suna kan farautar Janar  Tsige da ya jagoranci yunkurin juyin mulkin.

Yankin Amhara shi ne na 2 mafi girma a Habasha bayan Oromo, yankunan da aka shafe shekaru biyu ana zanga-zangar adawa da gwamnati da tilastawa tsohon fira minister Hailemariam Desalegn yin murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI