Bakonmu a Yau

Isa Sunusi Manajan yada labaran Amnesty kan rahoton kungiyat da ya zargi Jami'an tsaro kan gallazawa jama'a

Wallafawa ranar:

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta yi zargin cewar har yanzu jami’an tsaro na gallazawa jama’a da kuma cin zarafin su ta hanyoyi daban daban.Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ya bayyana cewar da dama daga cikin irin wadannan mutane da aka ci zarafin su basa samun taimakon da ya dace koda sun kai kara a wajen shugabannin jami’an tsaron da kuma kotuna.Daraktan kungiyar a Najeriya, Osai Ojigho ta ce duk da dokar kasar na haramta azabtar da mutane da kuma kafa kwamitin sake fasalin rundunar SARS, har yanzu ana samun matsalar.Dangane da wannan rahoto, mun tattauna da Isa Sanusi, Manajan yada labaran, kungiyar kuma ga abinda yake cewa game da rahotan.

Tambarin kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International
Tambarin kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International Amnesty