Nijar-Boko Haram

Ta'addanci ya hallaka fararen hula 140 cikin watanni 5 a Diffa

Wasu 'yan gudun hijira da suka tsallakewa hare-haren kungiyar ta Boko Haram
Wasu 'yan gudun hijira da suka tsallakewa hare-haren kungiyar ta Boko Haram REUTERS/Afolabi Sotunde

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce, sama da mutane 140 ne suka rasa rayukansu a cikin watanni 5 din farkon wannan shekara a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar gab da iyakar kasar da Najeriya mai fama da rikicin kungiyar Boko Haram. 

Talla

Cikin rahoton mako-mako da ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya ce Tun cikin watan maris din da ya gabata kawo yau hare haren mayakan Boko Haram kan fararen hula sun yawaita, inda ya lakume rayukan akalla fararen hula 140, matakin da ke nuna yawaitar mutanen da rikicin ke hallakawa idan aka kwatanta da bara.

Rahotan ya bayyana cewa hare-haren baya-bayan nan da Boko Haram ta kai a ranakun 18 da 19 ga wannan wata na Yuni kan kauyuka da dama  ajihar ta Diffa sun haddasa asarar rayukan fararen hula akalla 6 baya ga tilastawa daruruwa yun hijira zuwa jihar Bosso da ke gabar tabkin Tchadi

A bangare guda kuma rahoton ya bayyana cewa, hare-haren watan Maris ya hallaka karin fararen hula akalla 88 duk dai a jihar ta Diffa wadda ke matsayin tinga ko kuma mashigar mayakan na Boko Haram daga Najeriya.

Babbar Jami'ar hukumar jinkai ta Majalisar Dinkin duniya a kasar ta Nijar Fatouma Bintou Djibo, ta bayyana yawaitar hare-haren a matsayin babban abin takaici kuma kalubale ga tsaron kasashen na yammacin Afrika.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniyar ya nuna cewa daga 2015 zuwa yanzu hare-haren ta'addancin na Boko Haram ya tilasta yawaitar 'yan gudun hijira a jihar ta Diffa zuwa adadin akalla dubu 3.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI