Najeriya - Abuja

Batutuwan tsaro da kudin bai daya sun mamaye taron ECOWAS a Abuja

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin taron ECOWAS a birnin Abuja. 16/12/2017.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin taron ECOWAS a birnin Abuja. 16/12/2017. FEMI ADESINA

An soma taron shugabannin kungiyar kasashen yammacin nahiyar Afirka ECOWAS a birnin Abuja, Najeriya.

Talla

Manyan batutuwan da taron zai mayarda hankali akai sun hada da, halin da tsaro ke ciki a yankin na Yammacin Afirka, shirin samar da takardar kudin bai daya tsakanin kasashen na ECOWAS, da kuma rikicin siyasar kasar Guinea Bissau.

Sauran batutuwan ta taron na ECOWAS zai tattauna akai sun hada da dumamar yanayi, da kuma gina matasa.

Idan za a iya tunawa, a watan Afrilu na shekarar 2012 aka kafa tawagar wakilan kasashen yammacin Afrika ciki harda rundunar sojin hadin gwiwa, karkashin shirin ECOMIB, domin samar da tsaro a Guinea Bissau, tabbatar da doka da oda, da kuma sansanta rikicin siyasar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI