Isa ga babban shafi
Libya-Turkiya

Mu na gab da fara farmakar jirage da kadarorin Turkiya- Haftar

Khalifa Haftar babban kwamandan Hafson sojin kasar Libya wanda ke rike da galibin manyan yankunan kasar
Khalifa Haftar babban kwamandan Hafson sojin kasar Libya wanda ke rike da galibin manyan yankunan kasar Reuters
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Babban Hafson Sojin Libya mai karfin fada aji da ke riko da galibin yankunan kasar Khalifa Haftar ya bukaci sojojinsa, su farmaki jiragen ruwa da sauran kadadrorin kasar kasar Turkiya, bayan zargin da ya yin a cewa Turkiya na agazawa bangaren gwamnati mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.

Talla

Kakakin Haftar, Janar Ahmad Al-Mesmari ya ce yanzu haka sojin saman kasar ta Libya a shirye su ke su fara farmakar kanana da manyan jiragen ruwan Turkiya da ke kai kawo a mashigar ruwan kasar baya ga manyan kadarorinta.

Akwai dai jita-jitar da ke bayyana cewa, Turkiya ta tallafawa gwamnatin Firaminista Sarraj da Makamai don yakar Haftar wanda ya kaddamar da farmakin fara kwace iko da birnin Tripoli cikin watan Aprilu.

Fada dai ya dawo sabo ne a kasar ta Libya mai fama da rikici tun bayan da Haftar mai rike da galibun yankunan kasar ya fara yunkurin kwace iko da birnin Tripoli cikin watan Aprilu duk kuwa da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarori 2 masu rike da makamai a kasar.

Tun bayan juyin juya halin da ya hambarar da shugaba Mu'amar Gaddafi a shekarar 2011 ne kasar Libya ta fada rikici da ya kai ga hallakar tarin jama'a baya ga tserewar wasu don gudun hijira inda a bangare guda kuma ake zargin cewa rikicin ya yi sababin bazuwar makamai tare da haddasa tashe-tashen hankula a kasashen Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.