ECOWAS

ECOWAS ta amince da ECO a matsayin sunan kudinta na bai-daya

Yayinda ECOWAS ta amince da ECO a matsayin sunan kudinta na bai-daya, wasu masana sun bukaci kasashen kungiyar su karfafa kudaden kasarsu.
Yayinda ECOWAS ta amince da ECO a matsayin sunan kudinta na bai-daya, wasu masana sun bukaci kasashen kungiyar su karfafa kudaden kasarsu. AFP Photo/ISSOUF SANOGO

Kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ta amince da matakin sanya sunan ECO ga takardar kudin bai-daya da kasashen yankin za su rika amfani da shi, daga watan Janairu na shekarar 2020.

Talla

Shugabannin kasashen na ECOWAS sun cimma matsayar ce, yayin taron da suka yi jiya asabar a Abuja, babban birnin Najeriya.

Taron ya kuma baiwa cibiyar hada-hadar kudaden yammacin Afirka da kuma manyan bankunan kasashen yankin, umarnin soma aikin aiwatar da shirin fara amfani da kudin na bai-daya kamar yadda aka tsara.

Yayin taron na ECOWAS kashi na 55, Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou, ya karbi ragarmar jagorancin kungiyar daga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Sauran manyan batutuwan da taron na ECOWAS ya mayarda hankali akai sun hada da, halin da tsaro ke ciki a yankin na Yammacin Afirka, rikicin siyasar kasar Guinea Bissau, dumamar yanayi, da kuma gina matasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI