Sudan

Daular Larabawa ta nemi sulhu tsakanin Soji da farar hula a Sudan

Daruruwan masu zanga-zanga a birnin Khartoum na kasar Sudan
Daruruwan masu zanga-zanga a birnin Khartoum na kasar Sudan REUTERS/Umit Bektas

Dai dai lokacin da jagororin masu zanga-zanga ke kiran gagarumin bore don bijirewa shugabancin mulkin soja a kasar, a bangare guda kuma gwamnatin mulkin Sojin ke sake nuna yatsa ga jagororin farar hula, Hadaddiyar Daular Larabawa ta bukaci dorewar tattaunawar fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.

Talla

Cikin sakon da ministan harkokin wajen Daular Larabawan Anwar Gargash ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce rikici ba zai kawo karshen matsalar da Sudan ke fuskanta ba, face an zauna an tattauna tare da samar da mafita ga halin da kasar ta Tsunduma.

Bayan zanga-zangar ranar Lahadi da ta haddasa mutuwar mutane 10 tare da jikkatar wasu da dama a kasar ta Sudan, duk kuwa da gargadin gudanar da ita da gwamnatin Sojin ta yi, yanzu haka jagororin masu zang-zangar sun bukaci gudanar da wani gagarumin Bore a ranakun 13 da 14 ga watan nan.

A cewar bayanan na Gargash dole ne bangarorin biyu su sulhunta rikicin da ke tsakaninsa tare da raba mukamai ko kuma mika mulki dai dai da tanadin doka.

Bangarorin biyu dai na ci gaba da dora alhaki kan juna game da yadda mutane da dama ke ci gaba da rasa rayukansu a kowacce zanga-zanga da aka shirya.

Ko a baya bayan dai sai da kasashen Habasha da kungiyar Tarayyar Afrika suka mika wani jadawalin shawarwari ga gwamnatin Mulkin sojin ta Sudan don ganin an warware rikicin da kasar ta Tsunduma tun bayan hambarar da shugaba Omar Hassan al-Bashir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI