Isa ga babban shafi

Magajin garin Daura ya kubuta daga masu garkuwa da mutane

Magajin garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, siriki ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Magajin garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, siriki ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari NAN
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 min

A Najeriya, Magajin garin Daura kuma sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Musa Umar Uba ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane yau Talata bayan shafe tsawon watanni 2 a hannunsu.

Talla

Hadimin shugaban Najeriyar ta fannin kafofin yada labarai na zamani Bashir Ahmad ne ya wallafa batun nasarar ceto magajin garin na Daura a shafinsa na Twitter, inda ya ce lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata.

Tun a ranar 1 ga watan Mayun da ya gabata ne, wasu ‘yan bindiga 4 suka sace Alhaji Musa Umar Uba, magajin garin na Daura, mahaifar shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari.

Rahotanni sun ce an yi nasarar ceto Alhaji Uba ne bayan wani artabu tsakanin ‘yan bindigar da Jami’an tsaro a cikin garin Kano da ke makwabtaka da jihar ta Katsina inda aka yi garkuwa da Basaraken.

Cikin sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta fitar ta bakin kakakinta, SP Gambo Isa ta ce an yi nasarar ceto Basaraken Alhaji Uba cikin koshin lafiya.

Sanarwar ta ‘yan sandan Katsina ta taya murna ga daukacin al’ummar garin na Daura da ma jihar ta Katsina baki daya, sai dai ba ta fayyace ko kai tsaye an kai basaraken masarautarsa ba ko a a.

Basaraken wanda tsohon Kwanturola ne na hukumar Kwastam mai yaki da fasakwauri a Najeriyar miji ne ga ‘yar uwar shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.